Ana fargabar mutuwar mutane da dama bayan ruftawar ƙasa a Kano

Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu bayan wani ramin yashi da ake hako tubali ya rufta a kauyen Ridawa da ke karamar hukumar Ghari a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba yayin da ma’aikata ke aikin hako rami mai zurfi domin yin tubali, inda ramin ya rufta kwatsam ya binne wasu daga cikinsu.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya janyo firgici, inda mazauna yankin da abokan aikin suka garzaya domin ceto wadanda suka makale.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ghari/Tsanyawa, Sani Bala, ya bayyana cewa rahotannin farko sun nuna kimanin mutane 10 na iya kasancewa a karkashin ramin, yana mai kira ga hukumomi da su gaggauta kawo kayan aikin ceto na musamman.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto, yayin da ake kokarin tono wadanda suka makale, amma har yanzu da dama ba a ceto su ba, lamarin da ke kara tsananta fargabar yawan mace-mace.

Mazauna yankin sun ce irin wannan hadari ba bakon abu ba ne a wuraren hako tubali na karkara, inda galibi ake aiki ba tare da ingantattun matakan tsaro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *