Ana Zargin Jami’an Hukumar Kwastan A Katsina Da Karbar Haraji Ga Danyar Gyada A Wurin Masu Safararta

Da alamu dai masu sana’ar saye da sayar da danyar gyada da ma masu sarrafa ta domin yi kuli-kuli da mai a jihar Katsina na dab da shiga wani mawuyacin hali domin kuwa jami’an hukumar kwastan sun fara waiwayo su.

A binciken da Jakadiya TV ta gudanar, ta gano cewa jami’an kwastan din sun soma tarbe masu safarar gyadar musamman daga kasuwannin Dankama da Kaita da Kagadama zuwa sauran sassan jihar inda suke amsar makudan kudade daga hannun su a matsayin harajin duti.

Jakadiya TV ta zanta da wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa kai tsaye, Abubakar Idris Kankara, wanda muka iske a kasuwar Dankama da Alhaji Bishir Rahamawa mai injinan sarrafa gyadar inda suka yi mana karin haske dangane da wannan matsala da ta kunno kai kwanannan.

Sun ce jami’an kwastan din na karbar nera dubu 10 zuwa daga masu motocin J5 da nera dubu 60 zuwa sama daga masu manyan motoci da ke dauke da gyadar kuma babu wata takarda ko shedar da ake ba su.

Ita ma wata dattijiya da ke sana’ar sarrafa gyadar domin yin kuli-kuli da mai, Nana Ali, ta koka a kan wannan matsala da ke niyyar saka su da iyalan da suke kulawa da su cikin halin La’ilaha’ula’i.

Ta ce yawancin matan da ke amfani da gyadar wajen yin kuli-kuli da mai suna yin sana’ar ne domin kulawa da marayun da mazajen su suka mutu suka bari kuma barin sana’ar zai taba rayuwar marayun ta fuskar abinci da kiwon lafiya da karatu da sauran bukatun yau da kullum.

A kasuwar Dankama mun iske direbobin motocin jigilar gyadar da leburorin da ke lodin gyadar sun yi cirko-cirko inda suka bayyana mana cewa hanya ba ta biyuwa sabo da tsoron haduwa da jami’an kwastan.

Alhaji Babayye da Alhaji Bala K. Galma direbobi ne, sai Abubakar Idris, wanda shi kuma lebura ne kuma kowannen su ya fada mana yadda wannan matsala za ta shafi neman abincin sa.

Lebura Abubakar Idris ya ce a matsayin su na matasa masu jini a jika sun zabi su yi aikin karfi ne domin biyan bukatun su a maimakon daukar abin wani ko aikata abin da bai dace ba a cikin al’umma.

Da Jakadiya ta nemi jin ta bakin hukumar kwastan ta jihar Katsina dangane da wannan lamari, jami’in ta na hulda da jama’a, Tukur Balarabe, ya ce kwantarolan hukumar na jiha ya rigaya ya yi magana a wasu kafafen yada labaru kuma ba zai yin wata magana ba.

Idan dai har wannan lamari ya ci gaba a haka, toh lallai akwai yiwuwar dubban jama’a za su kara shiga halin matsin tattalin arziki da jin dadi tare haddasa karuwar rashin aikin yi da aikata laifukka a jihar Katsina.

Don haka akwai bukatar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su nemo hanyoyin warware wannan matsala kafin ta ta’azzara domin ci gaban kowa da kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *