Atiku Ya Sha Alwashin Samar Da Ƴan Sandan Jihohi Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Abubakar Atiku, ya yi alkawarin samar da ‘yan sandan jihohi idan yayi nasara a zaben 2023.

Ya ce hakan zai tabbatar da magance matsalolin tsaro a kasar nan.

Atiku ya yi wannan alkawarin ne jiya Asabar a Benin, lokacin yakin neman zabensa a jihar Edo.

Atiku ya ce gwamnatinsa za ta hada kan kasar nan ne ta hanyar baiwa kowane bangare ra’ayin zama na kowa, yana mai cewa, ba za a cire wani bangare ba.

Ya ce zai maido da tsaro a kasar nan ta hanyar tabbatar da cewa an samu karin jami’an ‘yan sanda a kan tituna tare da samar musu da kayan aiki zai taka muhimmiyar rawa kan wannan hali da Najeriya ke ciki.

A nasa bangaren, Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce Atiku na da kyau ga Najeriya kuma zai ceto al’ummar kasar daga yunwa.

A halin da ake ciki, Atiku ya ce zai fara rangadin jihohin da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa a shiyyoyin kasar nan shida a ranar Talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *