Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU, ta sake shigar da kara na neman a soke hukuncin da kotun masana’antu ta kasa da ta yanke hukuncin na cewa malaman jami’o’in su koma aji. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana, SAN ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da wasu manema labarai a babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar.
A baya cewa Mai Shari’a Hamman Polycarp na Kotun Masana’antu a ranar 21 ga Satumban wannan shekarar, ya umarci malaman da ke yajin aiki su koma bakin aikin su.
Amma ASUU ta shigar da kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, da nufin yin watsi da hukuncin kotun na masana’antu.
Sai dai kotun daukaka kara ta bayyana cewa ba za ta saurari karar da ASUU ta shigar ba idan kungiyar ta kasa yin biyayya ga hukuncin karamar kotun.
Kotun daukaka kara, a ranar 7 ga watan Oktoba, ta umarci malaman da suka yajin aiki da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
An dakatar da yajin aikin na watanni 8 ne a ranar 14 ga watan Oktoba. Kuma An ci gaba da gudanar da harkokin ilimi gaba daya a wasu jami’o’in gwamnati yayin da wasu kuma suka shirya komawa kwanaki kadan masu zuwa.
Falana ya bayyana cewa, a jiya ne aka kammala hada kundun shigar da sabon karar, jim kadan bayan sanar da janye yajin aikin da aka jima ana yi.
Ya ce, duk da haka, “ba a sanya ranar sauraron karar ba tukuna”.
