Gwamnatin Buhari Za Ta Mayar Da Wani Katafaren Asibiti Zuwa Na Koyar Wa A Jigawa

Gwamnatin Buhari Za Ta Mayar Da Wani Katafaren Asibiti Zuwa Na Koyar Wa A Jigawa

 

Gwamnatin tarayya ta karbi asibitin koyarwa na Reshid Shekoni dake birnin Dutse a jihar Jigawa.

Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire da Gwamnan Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar ne suka sanya hannu akan takardar yarjejeniyar.

Yarjejeniya ta kunshi mika asibitin koyarwa ga Jami’ar Tarayya dake birnin Dutse.

A jawabinsa wajen bikin sanya hannu da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce rattaba hannun, babban tarihi ne ga jihar Jigawa.

A cewarsa hakan zai kara inganta harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar.

Tun da farko, Jami’ar Tarayya ta Dutse ta fara ayyukan koyarwa da horar da dalibanta a asibitin.

Yayin da sanya hannu kan yarjejeniyar ta nuna cewar an kammala aikin kar’bar asibitin baki d’aya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *