Ba Gaskiya Bane Batun Gwanjon Dubban Motoci Da Muka Damƙe Daga Mutane – Kwastam

Ba Gaskiya Bane Batun Gwanjon Dubban Motoci Da Muka Damƙe Daga Mutane – Kwastam

Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Najeriya ta ƙaryata labaran da ke yawo cewa nan ba da jimawa ba zata yi Gwanjon Motoci 7000 data ƙwace daga Mutane.

Mataimakin Kwanturola kuma Kakakin Hukumar Timi Bomodi, ya bayyana a cikin takarda da ya rattabawa hannu a Madadin Kwanturola-Janar na Hukumar Hana Fasa Ƙwauri, ya bukaci ƴan Najeriya da su riƙa ziyartar yanar gizo da aka ware don yin Gwanjon tare da samun sahihan bayanai akan lokacin da zata yi Gwanjon.

Yace yin Gwanjo ta hanyar yanar gizo itace hanya ɗaya tilo da Hukumar take amfani da’ita domin yin Gwanjo ga Al’umma.

“Tun lokacin da muka ƙaddamar da shafin, zai tabbatar da adalci ga hanyoyin da za’a bi domin yiwa Al’umma Gwanjo.

Yace dole sai mutum ya gabatar takardar biyan shaidar biyan kuɗin haraji da Hukumar kula da tattara kuɗaɗen Haraji ke badawa, tare da haɗawa da Email.

 

Bomodi ya kara da cewa dole ne masu bukata su cika wadannan sharuddan kafin a karbe su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *