Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari
Jam’iyyar APC Mai Mulki ta rasa jaha daya da take da iko akanta, Cigaban zai ƙarawa Abokiyar hamayyarta wato jam’iyyar PDP ƙarfi, domin tunkarar Babban zaɓen Shekarar 2023.
A yayin da aka Kammala zaɓen, Dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Ademole Adeleke an ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar Zama Zaɓaɓɓen Gwamnan Jahar Osun.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa, ofishin tattara bayanai na jahar Osun dake Osogbo a safiyar ranar lahadi, ta sanar da cewa Adeleke ya samu nasarar lashe zaben da ya gabata a ranar Asabar, inda ya samu kuri’a 403,371.
A zaben Shekarar 2018, zababben Gwamnan ya taɓa shan kaye ga Gwamna Adegboyega Oyetola, Amma bayan shekaru 4 ya dawo domin kora abokin Takarar nasa daga kan karagar mulki, wanda yake da ƙuri’u 375,027.
Duk da cewa, jam’iyyu 15 ne suka fafata a zaɓen, Amma jam’iyyu 2 ne, suka fi karfi a fafatawar , wanda ya kasance tsakanin jam’iyyar APC da PDP.
Zaben jahar Osun shine zabe na karshe, kafin zuwan Babban zaben Shekarar 2023 Wanda shine zai saka manyan jam’iyya su gwada ƙarfin su kafin Babban zaɓe.
Yanzu Jam’iyyar PDP tana da iko akan wata jaha yankin kudu maso yamma kamar yadda ta samu nasarar lashe zaben jahar Oyo a zaben Shekarar 2019.
