Zargin badakalar kuɗade: A ƙarshe dai ICPC za ta gurfanar da El-Rufa’i a gaban kotu

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta sanar da cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, a gaban kotu a ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2026, bisa wasu zarge-zargen da suka shafi almundahana.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa za a fara shari’ar ne a babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ake tuhumar El-Rufa’i da laifukan da suka haɗa da karkatar da dukiyar gwamnati da kuma almundahanar kuɗi.

Haka kuma, ICPC ta ƙara da cewa akwai wata ƙara daban da aka shigar a babbar kotun jihar Kaduna, wadda ta ƙunshi zarge-zargen cin zarafin ofis da zamba.

Hukumar ta jaddada cewa ta bi dukkan matakan da doka ta tanada, tare da tabbatar da cewa an riga an miƙa takardun gayyata ga El-Rufa’i kafin fara shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *