Engr Nura khalil Dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP yace a halin yanzu babu Wanda yakamata a tausayama sama da talakawa.. saboda halin suka tsinci kansu a jihar katsina kullun talauci yanata karuwa ,gashi matasa Babu aikinyi ,ta’addanci yanata Kara samun wuri.
Bisa Lura da nayi akan matsalolin katsina ta Samo asali daga matasa marassa aikinyi Wanda sunyi karatu Amma zaune suke gida gashi Babu wani jari ko tallafi da zai tamakesu su Fara wata Sana,a wadda zata rage masu radadin zaman da suke.
Duk inda kashiga yanzu a katsina zakaga majalissar matasa wasu tundaga safe har zuwa dare suna zaune saboda Babu aikinyi ko Sana,a Sai gardama daganan wadda take jawo fadace fadace, talauci Yana jefa mutane dayawa su aikata abinda ba halayyarsu bace, talauci zai iya canza ma mutun tunani acikin kankanin lokaci, talauci masifa neh Kuma shine tushen matsalolin kasar mu.
Idan har Allah ya bamu gwamnati zamuyi kokarin bama matasa aiki ,zamu kirkiri hanyoyin da matasa zasu rika samun kudi ko da gwamnati Bata Basu aiki ba ta hanyar koyar da sana’oi ,zamuyi kokarin mu akan Sha,anin tsaro da tallafama Wanda masifar ta fadamawa kamar wadanda ke kiwo aka sace abun kiwon ,da Wanda suka dogara da noma Amma noman ya gagaresu domin a wajen mu sunada mahimmanci ko ince suma kadarori ne a jihar mu.
Muna barar addu,ar ku al’ummar jihar katsina tare da abokin takara ta Engr muttaqa rabe darma da ku sanyamu addu’a Allah yabamu ikon aiwatar da kyakkyawan nufin mu dake a zuciya.
Rubutun:Abubakar Usman
