Bayan Kwanaki 3, A Karshe INEC Ta Mikawa Adeleke Shaidar Lashe Zaɓen Gwamnan Osun

A yau Laraba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke.

Kafin mika takardar shaidar ga Adeleke da Kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Osun, Ogun da Oyo, Farfesa Kunle Ajayi, ya gabatar da shi ga zababben mataimakin gwamnan jihar, Prince Kola Adewusi.

Gabatarwar ta zo ne kimanin sa’o’i 72 bayan bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli shekarar nan, inda ya samu kuri’u 403, 371, wanda ya doke Mista Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC mai mulki, da ya samu kuri’u 375,027.

A jawabinsa na karbar takardar shedar a wani dan takaitaccen biki da aka gudanar a babban ofishin INEC dake Osogbo, Adeleke ya sadaukar da nasararsa a zaben domin tunawa da babban yayansa, Sanata Isiaka Adeleke da al’ummar jihar Osun baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *