Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Ƙungiyar Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya wato (ALGON) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya data yi gaggawar kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’oi ta ƙasa keyi.
Ƙungiyar tayi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar Bayan taro, a ƙarshen taronsu karo na 32 na Shuwagabannin Ƙungiyar, wanda ya wakana a Lokoja babban birnin Jihar Kogi.
Sanarwar Bayan taron, ta samu sa hannun Shugaban Kungiyar na jihar Borno Hon. Ali Umaru Baroli da shugaban kungiyar na jihar Imo Willi TC Okoliegwo da kuma shugaban kungiyar na jihar Ogun Hon. Babatunde Emilola-Gazal
Kungiyar shuwagabannin kananan hukumomin ta bayyana cewa, ta damu ƙwarai tare da jaje ga Ɗalibai da iyaye da kuma sauran al’umma akan cigaba da dogon yajin aikin da kungiyar malaman jami’oi keyi, wanda ke kara haifar da kunci ga Al’umma.
Kungiyar malaman jami’oin ta kasance cikin yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabarairu wanda ta kira da gazawar gwamnati na cika yarjejeniya tsakaninta da Malaman Jami’o’i.
Kungiyar shuwagabannin kananan hukumomin ta kuma bayyana cewa akan Babban Zaɓen shekarar 2023, a shirye take ta goyi bayan duk Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa dake da shirin baiwa Ƙananan Hukumomi gashin kansu.
Sanarwar wacce aka fitar tace ” Shuwagabancin Ƙungiyar ALGOn ta kasa, tana goyon bayan shirin samar da Ƴan Sandan Al’umma, a matsayin wata dubara ta samar da ingantaccen tsaron rayuka da Dukiyoyin Al’ummar Ƙasa.
