DSS sun kubutar da sakataren ƙaramar hukumar Kibiya tare da kama waɗanda su ka yi garkuwa da shi

Jami’an hukumar tsaron farin kaya na DSS sun kama wadanda suka yi garkuwa da Sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya a Kano Hon. Hamza Musa Durba inda suka kuɓutar da shi kamar yadda jaridar Arewa Updates ta rawaito.

Bayanan da Arewa Updates ta samu sun nuna cewa jami’an sun kubutar da sakataren ne a wani daji da ke Kibiya bayan da aka soma tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da shi ta waya.

Jamiʼan sun kama 2 daga cikin inda aka same su da bindiga ƙirar Ak47.

Ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *