Tinubu ya jagoranci taron Majalisar ‘Yan Sanda, don tabbatar da Disu matsayin Sufeto Janar

Shugaban ƙasa Bola Tinubu na jagorantar taron Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock Presidential Villa, domin kammala matakan tabbatar da muƙamin sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.

Ana sa ran taron zai tabbatar da naɗin Mukaddashin Sufeto Janar, Tunji Disu, a matsayin cikakken Sufeto Janar (IGP), bayan murabus ɗin tsohon IGP Kayode Egbetokun.

Taron da aka fara da tsakar rana a ranar Litinin an kira shi ne domin amincewa da sunan Disu bisa tanadin Dokar ‘Yan Sanda ta 2020, kafin a tura sunansa zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa ta ƙarshe. Daga cikin mahalarta taron akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ibrahim Gaidam, da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, tare da gwamnonin jihohi 36 da sauran mambobin majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *