Najeriya na fama da rashin kulawar cututtukan zubar jini

Yayin da duniya ke rungumar maganin kwayoyin halitta (gene therapy), Najeriya na fama da rashin kulawar cututtukan zubar jini masu tsanani

Najeriya na ci gaba da fama da ƙarancin magunguna da kayan gwaji ga masu fama da cutar haemophilia, yayin da ƙasashe masu ci gaba ke amfani da sabbin hanyoyin jinya na gene therapy da ke ba marasa lafiya damar samar da sinadarin daskare jini da kansu.

A cewar bayanan Ƙungiyar Duniya ta Masu Cutar Haemophilia (World Federation of Haemophilia), ana hasashen mutum ɗaya cikin 10,000 na haihuwa na rayuwa na ɗauke da cutar, lamarin da ke shafar kusan mutum 465,000 a duniya baki ɗaya.

A wani gida da ke Kaduna, wani ma’aurata sun rada wa ɗansu na uku suna Onwuzueike, ma’ana “mutuwa ta dakata,” bayan sun riga sun binne ‘ya’ya maza biyu kafin su kai shekara goma—ɗaya sakamakon haɗarin babur, ɗaya kuma bayan tiyatar ido mai sauƙi. Daga baya aka gano cewa ba la’ana ba ce, illa cutar Haemophilia A, wadda ke faruwa sakamakon ƙarancin sinadarin “Factor 8” a jini, abin da ke sa rauni ƙanƙani ya zama barazana ga rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *