Duk Da Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Zata Gina Gadoji, Hanyoyi A Ƙananan Hukumomi 4 Da Miliyan 700
Gwamnatin Zamfara a ranar Juma’ar nan ta ce ta ware Naira miliyan 700 domin sake gina gadoji guda biyar da kuma tituna a fadin kananan hukumomi hudu.
Kwamishinan ci gaban al’umma, Alhaji Abdullahi Gurbin-Bore ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da ayyukan da aka gudanar a Burgediya ta 1, Kantonment na Sojojin Najeriya da ke Gusau a Jihar Zamfara ranar Juma’a.
Kwamishinan ya lissafo gadojin da suka hada da kauyen Maigungumi da kauyen Tofa dake kusa da Dansadau, karamar hukumar Maru; gadar kauyen Badoki, gadar Gurusu da Nasarawa Bukulu a karamar hukumar Bukuyum, da kuma gadar Ruwan Gora da ke yankin Talata Mafara.
Aikin ya kuma hada da hanyar shiga makarantar Staff School of 1 Brigade mai tsawon mita 500, da ke Gusau
