Dukkanin Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa Sun Karya Dokar Zaɓe A Taron Lauyoyi – Kingsley

Wani mai rajin tabbatar da shugabanci na gari, Kingsley Wali, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, Peter Obi da Kashim Shettima sun karya dokar zabe a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA).

Wali ya ce ’yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, da Labour (LP) da kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC sun mayar da taron wurin yakin neman zabe.

Shettima, Sanatan Borno ta tsakiya, ya wakilci mai rike da tutar takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu a wajen taron NBA da aka gudanar a Legas a farkon makon nan.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa Ya shaida wa manema labarai cewa abin mamaki ne ganin yadda ‘yan siyasa masu neman shugabancin Najeriya suka yi hakan a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta hana yani neman zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *