Hukumar yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Antoni Janar na ƙasa (AGF), Abubakar Malami, tare da matarsa, Asabe Bashir, da ɗansa, Abdulaziz, kan zargin aikata laifin badakalar kuɗi.
An gurfanar da su ranar Juma’a a gaban Joyce Abdulmalik, alkaliyar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan sauya alƙalin da ke sauraron shari’ar.
A zaman kotun, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da shari’ar ta zo gaban sabuwar alkaliyar, inda ya roƙi kotu ta karɓi amsar tuhumar daga bakin waɗanda ake zargi, alamar cewa shari’ar na shiga sabon babi mai cike da hankali da damuwa.
