Falana Ya Bayyana Dalilin Da Yasa ASUU Zata Janye Yajin Aiki Nan Bada Jimawa Ba

Babban Lauyan Najeriya, SAN, Femi Falana ya bayyana fatansa cewa za a janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi nan da kwanaki ba makonni ba.

Babban Lauyan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da littafi mai suna ‘Breaking Coconut With Your Head’ na Lanre Arogundade a yau Litinin a Legas.

Ya bayyana cewa akwai yiwuwar a janye yajin aikin a wajen kotun, inji jaridar Tribune.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *