Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kammala rajistar sa ta yanar gizo a matsayin mamba a jam’iyyar ACCORD, domin bin sabuwar Dokar Zabe ta 2026 wadda ta wajabta wa jam’iyyun siyasa su rika adana rajistar mambobinsu a tsarin dijital.
Matakin na cikin kokarin tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da cikakken bayanan mambobinsu a tsarin zamani, kamar yadda dokar ta tanada, domin inganta gaskiya da kuma saukaka bincike kan sahihancin mambobin jam’iyya a fadin kasar.
