Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaben 2026 da su yi murabus daga mukamansu kafin ranar 31 ga Maris, 2026.
Umarnin ya fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Tofa, ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce an isar da wannan umarni ne ta wata takardar hukuma da Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Ibrahim, ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, matakin ya yi daidai da tanadin sashe na 88(1) na dokar zabe ta 2026, wadda ta tsara yadda masu rike da mukaman gwamnati za su shiga harkokin siyasa.
Gwamnatin ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma daidaito tsakanin dukkan masu neman takara, tare da hana amfani da mukami wajen samun wata fa’ida ta siyasa.
Sanarwar ta ce dole ne duk wanda ke son tsayawa takara ya yi murabus ko ritaya, kafin ranar Talata, 31 ga Maris, 2026.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati da su yada wannan umarni tare da tabbatar da an bi shi yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki ya yi daidai da irin matakan da ake dauka a matakin tarayya da wasu jihohi, domin tabbatar da gaskiya da kauce wa anfani da mukami a harkokin zabe gabanin zaben 2027.
Dokar zabe ta tanadi cewa wasu masu rike da mukamai dole ne su sauka daga mukamansu kafin su shiga zaben fidda gwani ko babban zabe, domin tabbatar da daidaito da gaskiya a tsarin dimokuradiyya.
