Ɗan takarar gwamnan jahar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Engr. Nura Khalil ya ce gwamnatin da ke mulki yanzu a jahar Katsina ta fi birai barna.
Nura Khalil ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da ya yi mutanen Katsina mazauna Kano dangane da sha’anin neman kujerar mulkun jahar.
Ya ce duk wasu kadarori da suke na gwamnatin Katsina ne yawanci duk gwamnatin ta cefanar da su da nufin yin wasu abubuwan da ba su da mahimmaci sosai ga al’umma har ta kai ga babu sauran abinda ya rage banda makaratu da Asaibitoci, ya ce suma don ba a iya sayar da su.
Ɗan takarar gwamnan na NNPP ya ce wannan shine dalilin da yasa ya ke son al’umma su ba shi dama domin gyara duk wata barna da gwamnatin ta APC ta yi da ciyar da jahar gaba ta yadda zata shiga sahun sauran jahohi tsararrakinta.
