Gwamnonin Arewa Ku Yi Abinda Dikko Raɗɗa Na Katsina Ya Yi A Bangaren Tsaro – CNG

Kungiyar Gamayyar kungiyoyin mutanen Arewa CNG, shiyyar jihar Katsina ta yi kira ga Gwamnonin da ke yankin Arewacin Najeriya musamman wadan da ke da matsalar rashin tsaro a jihohinsu da su yi koyi da irin abinda Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ya yi wajen samar da runduna ta musammam da zata yaki yan ta’adda da ke addabar jihar.

Kodinetan CNG, a jihar Katsina, Habibu Ruma ne ya yi kiran a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kirawo a wannan Alhamis din domin jinjina ga gwamnan na Katsina bisa ga wannan namijin kokari.

Ruma ya ce, hakika abinda Dikko Raɗɗa ya yi abu ne mai kyau kuma hakan na nuni da cewa da gaske ya ke zai kawar da matsalar tsaro a fadin jihar.

Ya ce, samar da rundunar ta musammam mai dauke da zaratan dakarun matasa kimanin 1500 wata hanya ce da za a kawar da yan ta’adda cikin gaugawa a jihar.

Ya ce dole a yaba wa Gwamnan yadda bayan ba matasan horo ya kuma samar da motoci masu sulke guda 10 da kirar Hilux guda 70 da babura 700 duk don a yaki yan ta’adda da aikin ta’addanci.

Kodinetan ya ce wannan ba karamin abin a yaba ba ne, aka kuma yi kira ga sauran Gwamnonin yankin na Arewa da su yi irin wannan suma a jihohinsu.

Ya ce in ba haka ba akwai yiwuwar in wadan nan zaratan matasa suka kora yan ta’addan daga jihar katsina su shiga wata jihar da babu irin wannan tsarin domin su ci gaba da cin karensu babu babbaka.

A karshe ya yi kira ga gwamna Radda da ya kula da walwala da jin dadin dakarun rundunar ta musammam tare da kula da dukkan hakkokinsu domin su ji dadin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *