Harin Bam a Maiduguri: Tinubu ya gaza – Amaechi

Tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa, Chibuike Rotimi Amaechi, ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan tabarbarewar tsaro a ƙasar kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

Amaechi ya bayyana harin bam da aka kai a Maiduguri a matsayin gazawar shugabanci, yana mai cewa gwamnati ta kasa kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ya kuma zargi gwamnatin da rashin ɗaukar matakan gaggawa da ƙwarewa wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa hare-haren da ke ci gaba na nuna gazawa a tsarin shugabanci.

Sai dai ya jajanta wa al’ummar Borno State da iyalan waɗanda harin ya shafa, tare da jaddada cewa dole ne gwamnati ta ɗauki alhakin tabbatar da tsaron jama’a.

Amaechi ya kuma gargadi cewa ‘yan Najeriya ba za su yi shiru ba idan har ba a ɗauki matakin gaggawa kan matsalar tsaro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *