An samu ragin mace-macen mata a asibitoci a Najeriya – Rahoto

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen rage yawan mace-macen mata masu haihuwa a asibitoci, inda wani rahoton Ma’aikatar Lafiya na shekarar 2025 ya nuna an samu saukar adadin daga mata 904 a 2024 zuwa 460 a 2025. Rahoton ya danganta wannan ci gaba da kara yawan kwararrun jami’an lafiya, inganta tsarin tura marasa lafiya zuwa manyan asibitoci da kuma bunkasa ayyukan kula da lafiyar mata da yara kanana.

A bangaren inganta ayyukan kiwon lafiya, rahoton ya nuna cewa an samu karin kashi 86.3% na kwararrun jami’an lafiya tare da inganta horo kan karbar haihuwa. Haka kuma, yawan cibiyoyin da ke ba da kulawar haihuwa ya karu daga kashi 82.2% zuwa 86.5%, yayin da mata masu ciki da ke zuwa awon ciki akalla sau hudu suka karu daga kashi 22.2% zuwa 28.7%.

Rahoton ya kuma bayyana cewa shirye-shiryen gwamnati kamar CEmONC, SEMSAS da MAMII sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar mata, inda sama da mata 20,000 suka amfana kai tsaye. Haka kuma, motocin daukar marasa lafiya sun taimaka wajen kai dubban mata cibiyoyin lafiya cikin gaggawa, musamman a yankunan karkara da kananan hukumomi 124.

Sai dai duk da wannan ci gaba, rahoton ya nuna cewa matsalar mace-macen mata na ci gaba da zama kalubale a Najeriya, musamman a yankunan karkara. Bincike ya nuna cewa matsaloli kamar rashin ingantattun cibiyoyin lafiya na matakin farko, jinkirin kai mata asibiti da kuma wahalar sufuri, musamman a wurare kamar Makoko da Bariga a jihar Legas, na ci gaba da haddasa asarar rayukan mata yayin haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *