Hisbah A Jihar Jigawa Ta Damƙe Kwalaben Giya Sama Da 380

Hisbah A Jihar Jigawa Ta Damƙe Kwalaben Giya Sama Da 380

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ce ta damƙe kwalaben Giya 384 a Ƙaramar Hukumar Kazaure.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Hukumar Muhammad Sale Korau ya sanya wa hannu a ranar Litinin.

Ya ce jami’an Hukumar ƙarƙashin jagorancin kwamandan jihar Ibrahim Dahiru sun samu nasarar kama giya a kan hanyar Katsina zuwa garin Kazaure.

Korau ya ce an kama mutum ɗaya da laifin safarar giya a jihar.

Ya ce an mika wanda ake zargin ga Hukumar ƴan sanda domin gudanar da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya.

Sai dai ya yabawa al’ummar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da munanan ɗabi’u a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *