Yakin Ukraine Da Rasha: Amurka Ta Ba Ukraine Tallafin Dala Billiyan Daya

Kasar Amurka ta shelanta kai wa Ukraine sabon tallafin tsaro da ya kai na dala biliyan daya, wanda ya kasance tallafi mafi girma.

Ma’aikatar tsaro ta Pentagon, ta kuma jadda aniyarta ta samar da karin tallafi, da ya hada da makaman roka masu gudun wace misali wadanda suke taimaka wa sojin Ukraine kai hari a kan dakarun Rasha ta bayan fagen daga.

Tallafin ya kuma kunshi motocin assibiti masu sulke da sauran makamai da harsasai.

Tuni daman Amurkar ta bai wa Ukraine tallafin da ya kai na kusan dala biliyan tara tun bayan Rasha ta mamayi kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *