Hukumar kula da harkokin makamashi ta duniya, wato International Energy Agency (IEA), ta ce a shirye take ta dauki matakin gaggawa domin daidaita kasuwar danyen mai ta duniya, yayin da farashi ke kara tashi sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
Rahoton Bloomberg News ya bayyana cewa kasashen mambobin IEA na rike da sama da ganga biliyan daya na danyen mai a matsayin ajiyar gaggawa, wanda za a iya saki idan rikicin ya haddasa tangardar wadata. Farashin danyen mai na Brent ya ci gaba da tashi tun bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi nuni da yiwuwar daukar matakin soja kan Iran, lamarin da ya kara jefa kasuwannin makamashi cikin fargaba.
Ko da yake ana ci gaba da hakar mai a yankin, IEA ta ce jigilar mai ta mashigar ruwa ta Strait of Hormuz ta fuskanci babbar matsala. A Najeriya ma, matatar Dangote Petroleum Refinery ta sauya farashin fetur a matakin sito, yayin da gidajen mai a Abuja suka kara farashin famfo, sakamakon tsadar sauke kaya da karancin kayayyaki.
