Wani babban jami’in sojin Najeriya mai mukamin Manjo da wasu sojoji sun rasa rayukansu bayan da mayakan ISWAP suka kai jerin hare-hare kan sansanonin soji a Jihar Borno tsakanin daren 28 ga Fabrairu zuwa safiyar 1 ga Maris 2026, lamarin da ya sake nuna tsananin barazanar tsaro a Arewa maso Gabas.
Majiyoyi sun ce hare-haren sun shafi sansanonin da ke Mayanti, Gajigana da Gajiram, inda maharan suka yi amfani da manyan bindigogi, rokokin RPG da jirage marasa matuki dauke da makamai. An ce an yi artabu mai zafi na sa’o’i kafin dakarun su samu nasarar dakile su.
Rundunar Operation Hadin Kai ta tabbatar da cewa ta dakile hare-haren da aka kai a Mayanti, Gajigana da Gajiram, inda ta ce an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kwato makamai masu yawa, duk da cewa wani jami’i ya “biya farashin rai” a artabun. Sojojin sun ce an samu nasarar fatattakar maharan tare da taimakon jiragen sama, yayin da aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kulawar gaggawa.
