Ina Da Damar Da Zan Gayyaci Wanda Naga Dama – Wike Ya Yi Wani Shagube

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya caccaki wadanda ke sukarsa kan ya gayyaci wasu muhimman mutane zuwa kaddamar da ayyukansa a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da yake kaddamar da Cibiyar Duba lafiyar Zuciya da kuma Gwajegwajen cutar Daji a Fatakwal da akai wa Lakabi da Dr Peter Odili Cardiovascular and Cancer Screening Centre.

Ya kara da cewa, Duk wanda ke da buri kara karfin cutar hawan jininsa kan wannan mataki da ya dauka, yana da damar yin hakan.

Ya kuma bayyana cewa, “Wadanda suke tambaya na mai yasa ban gayyace su ba domin kaddamar da ayyukan nawa, za su gayyace Ni zuwa yankunan su? Ina da damar gayyatar duk wani mahalukin da na gadama domin kaddamar da ayyuka na.”

Ya cigaba da cewa, ” Ko a ranar Laraba Adams Oshiomole zai zo ya kaddmar da wasu ayyukana, Ranar Alhamis kuma Peter Obi zai zo ya kaddanar da ayyukana

“Inda kuma ranar Juma’a Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zo ya Kaddamar da Makarantar Horas da Aikin Lauya.”

“Kazalika a ranar Litini kuma Kwankwaso Zai zo ya kaddamar don haka na zabo wadanda nake ra’ayi ne, don haka idan kana son cutar hawan jini ta kama Ka to wannan kuma kai kasiyoma kanka”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *