Kotu Ta Sake Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamna Na APC A Jihar Taraba

Kotu Ta Sake Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamna Na APC A Jihar Taraba

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta soke zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da ya tsayar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a yau.

Idan dai za a iya tunawa, tun da fari, babbar kotun tarayya da ke Jalingo a jihar Taraba ta sauke shi daga mukaminsa na dan takarar gwamnan jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.

Kotunan biyu, a hukuncin da suka yanke, sun bukaci shugabannin jam’iyyar APC da su gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna a Taraba.

Baya ga bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14, kotunan sun bukaci dan takarar da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba a inuwar Jam’iyar.

Yayin da hukuncin farko da Kotun Jalingo ta yanke, ya fito ne daga hannun daya daga cikin masu neman tsayawa takara, Cif David Sabo Kente, yayin da kuma na Abuja, wanda aka zartar a yau ya fito ne sakamakon karar da dan majalisar dattawa mai wakiltar Taraba ta tsakiya, Yusuf A. Yusuf ya shigar.

Su biyun wadanda suka ce ba a gudanar da zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar a jihar ba, na mamakin dalilin da ya sa shugabannin jam’iyyar a matakin kasa suka ci gaba da bayyana Bwacha a matsayin wanda ya lashe zaben.

Babbar kotun tarayya da ke Jalingo ta kara dagula wa Sanata Emmanuel Bwacha lissafi a wani hukunci da ta yanke na tsige shi a matsayin Sanatan Tarayyar Najeriya biyo bayan karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kansa na ficewa daga jam’iyyar da ta kai shi matsayin.

Shugabannin jam’iyyar PDP na jihar sun maka shi kotu jim kadan bayan ficewarsa daga jam’iyyar zuwa APC.

Yayin da Bwacha, ya riga ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a Jalingo, sai dai har yanzu ba a bayyana ko zai daukaka kara ba a hukuncin na yau wanda ya gudana a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *