INEC Ta Ce Za Ta Ɗauke Ofisoshin Ta A Wuraren Da Ake Kai Masu Hari

INEC Ta Ce Za Ta Ɗauke Ofisoshin Ta A Wuraren Da Ake Kai Masu Hari

Shugaban hukumar zabe mai zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana cewa hukumar za ta murmure daga hare-haren da ake kai wa cibiyoyinta tare da gudanar da zaben 2023.

Yakubu, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin Majalisar kasa da ke binciken hare-haren da aka kai kan cibiyoyin Hukumar, sai dai ya yi gargadin cewa dole ne a daina kai hare-haren.

Ya ce hukumar ta shaida faruwar al’amura 50 a jihohi 15 tun daga shekarar 2019.

A cewarsa, an kai hare-hare takwas a shekarar 2019, 22 a shekarar 2020 da 12 a shekarar 2021 yayin da takwas aka rawaito a shekarar 2022.

Shugaban INEC ya bayyana cewa jihar Imo ce ke kan gaba da hari 11 sai Osun mai bakwai, sai kuma biyar a Enugu da Akwa Ibom, yayin da Abia da Cross Rivers suma suka samu hudu.

Ya kuma bayyana cewa an samu bullar guda biyu a jihohin Anambra da Taraba sannan daya a jihohin Bayelsa, Ondo, Legas, Borno, Kaduna da Ogun.

Ya sanar da cewa, yayin da INEC ke daukar matakai da suka hada da mayar da wasu ofisoshi daga yankunan da ba su da tsaro, tana kokarin yin amfani da fasahar zamani tare da hada kai da jami’an tsaro wajen yin duk abin da ya kamata don dakile hare-haren da ake kai wa cibiyoyinta.

Yakubu ya nanata cewa duk da alamun barazana ga zaben 2023 da kuma yawaitar hare-haren da masu aikata laifuka ke kaiwa cibiyoyinta, hukumar na da kwarin gwiwar cewa irin wadannan hare-haren ba za su hana gudanar da zaben ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *