Tsadar Fetur: Ana Amfani Da Keken Shanu Maimakon Mota Wajen Ɗaukar Kayan Amarya A Katsina.

Wasu matasa a jihar Katsina sun bayyana cewa yanzu tsadar man fetur ta sanya dawowa da amfani da keken shanu wajen ɗaukar kayan ɗakin amarya.

Matasan sun ce maimakon a je a ɗauki hayar mota ya kasance mutum sai ya biya kuɗi masu yawa da kila zasu kai kimanin dubu goma ko ƙasa ga haka kafin a kai mashi kaya gara a yi amfani da keken shanun don samun sauƙi.

Sun ce sauƙin da mutum zai samu zai iya amfani da kuɗin wajen magance wata hidimar.

Tun a shekarar 2023 da ta gabata ne dai yan Najeriya ke fama da tsadar man fetur ɗin da alokaci guda ya yi tashin gwauron zabi zuwa sama da 600 a duk lita ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *