INEC Ta Gindaya Wasu Sabbin Sharuɗɗa Ga Masu Yaƙin Neman Zaɓe

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, a ranar Alhamis, ta amince da bugawa da fitar da ka’idojin yakin neman zabe; da kuma kudaden zaɓe na jam’iyyun siyasa, dana ‘yan takara da masu neman takara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce hukumar ta gana ne a ranar Alhamis inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da wallafawa da fitar da ka’idojin, tare da tattaunawa kan nadin sakataren INEC.

“Hukumar ta amince da wallafawa da fitar da ka’idojin gudanar da taruka na siyasa da tsare-tsare da yakin neman zabe da kuma na kudade da kudaden zabe na jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da masu neman tsayawa takara.”

Okoye ya ce sakamakon haka ne hukumar ta INEC ta sanya wadannan takardu guda biyu a shafinta na yanar gizo da kuma shafukan sada zumunta yayin da za a mika kwafin ga jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya tunatar da jam’iyyun siyasa wajibcin su mika rahoton da ake bukata ga hukumar bisa tanadin sashe na 90(4) na dokar zabe ta 2022 da kuma takunkumin da ya dace na rashin yin biyayya ga sashe na 89(4) na zaben. Aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *