Rashin Wutar Lantarki A Katsina: Teloli Na Tsoron Karya Alƙawari

Wasu teloli a Jahar Katsina da ke Arewa maso gabashin Najeriya sun koka game ƙarancin wutar lantarki da ake fuskanta a jahar.

Wannan na cikin wani rahoto da musamman da kafar sadarwa ta Alfijir Radio ta haɗa inda aka jiyo telolin na alhinin rashin samun wadatacciyar wutar lantarki.

Kamar yadda suka ce aikin sana’ar ɗinki yanzu ta koma dole sai dai su yi amfani da janareto kuma ba kowa ke da ikon sayen babban janareton da zai iya yin aikin ba.

Wannan dai acewarsu yana iya zama sanadiyar rashin cika alƙawarin da suka ɗauka ga kwastomominsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *