An Bada Horo Kan Noman Dankalin Turawa A Cikin Gida

matsalar chanjin yanayi an horar da dalibai dabarun noman dankalin turawa a cikin gida: A Wani mataki na shawo kan lamarin chanjin yanayi Kungiyar inganta yanayin muhalli a jihar Katsina mai Suma Greenish Way Initiative Crew a turance wato GREWIC ta yunkuro domin bada horo a kan matakan shawo kan lamarin.

Bayar da horon wani shirine karo na farko na shekarar 2023/2024 na samar da kyakyawan yanayin muhalli dakeda taken zaburar da matasa maza da mata ta hanyar azasu a tafarkin samar da dauwamammen cigaba.

GREWIC ta bada horonne ga makarantun ‘yanmata guda uku, dasuka hada da makarantar Sakandiren ‘yanmata ta kwana dake Karamar hukumar hukumar Dutsinma wato GGSS Shema, da ta Karamar hukumar Kankiya wato GGSS Rimaye, dakuma ta Karamar hukumar Jibia wato GGSS Dutsin Safe.

Bayarda horon ya gudanane a makarantar Sakandiren ‘yanmata ta Katsina wato Government Girls College Katsina dake cikin birnin Katsina.

Waarda kan yasamu halartar daliban Makarantun kwanan uku da malamansu, da jami’ai daga ma’aikatar ilmi ta jihar Katsina da mambobin kungiyar ta GREWIC.

An koyar da mahalarta taron dabarun noman zamani, na yin noman Dankalin turawa a cikin gida ta hanyar amfani da buhu ko bokitin fenti na roba, domin bunkasa samar da abinci.

Jami’an kungiyar da suka hada da Abdullahi Muhammad, ya gabatar da kasida akan matakan magance matsalar chanjin yanayi, inda ya bayyana muhimmancin dasa itace a matsayin daya daga cikin hanyoyin shawo kan lamarin, a yayinda Kabir Sodangi ya gabatar da tasa makalar akan rungumar aiki noma a matsayin hanyar samarda abinci da bunkasa tattalin arzuki.

Sannan Kuma Safiya Yahaya Sodangi ta wayarda kan mahalarta taron akan rage zubarda shara, ta hanyar sarrafata domin samar da aikinyi, a sailinda Abdulaziz Salisu da sakataren kungiyar Umar Masari sun karkare bayarda horon da yin Kira ga malamai da daliban da sukaci gajiyar Shirin,dasu yada ilmin da suka samu ga ‘yanuwansu da basu samu damar halartar horonba.

  1. Jami’an sun bukaci mahalarta horon dasurungumi dabiar dasa itatuwa alokacin bukukuwan aure da haifuwa, da bikin murnar kammala karatu da tunawa da ranar zagayowar haifuwa a matsayin wani salo na inganta yanayin muhalli da magance matsalar chanjin yanayi da dumamarsa.
    Da suke gabatarda jawabi a madadin ma’aikatar ilmi ta jihar Katsina da makarantun da suka amfana da horon, Daraktan kiniyya Malam Lawal Maikudi, da matimakin daraktan kula da ingancin ilimi Muhammad Abdulaziz da Malama A’isha Shu’aibu ta GGSS Rimaye da Malam Abduljalil Ismail na GGSS Dutsin Safe, sun yaba da hangen nesan kungiyar GREWIC na gudanar da horon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *