Majalisar Wakilai Ta Buƙaci A Kamo Sabon Shugaban CBN Da Babban Akanta

Majalisa ta bukaci kamo sabon shugaban CBN da babban akanta na kasa:

Kwamitin koken al’umma na Majalisar dokokin tarayyar Nijeriya ya gabatar da kudurin gurfanar da sabon shugaban babban Bankin kasa CBN Mr. Olayemi Cardoso, da babbar akantar Nijeriya Mrs. Oluwatoyin Madein da sauran mutane goma shabakwai.

Hakan yabiyo bayan kin amsa goron gayyatar da kwamitin, da keyin bincike akan yadda suke gudanar da ayyukansu.

Shugaban kwamitin Michael Irom, Ya bukaci babban sufeton Y’ansandan Nijeriya daya kamo dakuma gurfanar da mutanenen agaban zaurennan majalisar Kuma a gaban shugaban majalisar Tajudden Abbas, kafin ranar shahudu ga Watan shabiyu na shekarar da ake ciki ta 2023.

Majalisar ta cimma matsayar hakanne biyo bayan kudurin da Fred Agebedi ya gabatar a gaban zauren majalisar a ranar talata 5/12/2023.

Danmajlisar yace, cimma wanna matsayar, yabiyo bayan kin amsa goron gayyatar kwamitin majalisar da jami’an sukayi har sau hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *