RAHOTO
Wasu alummomi kenan mazauna Unguwar Gachi a cikin ƙaramar hukumar Kankia da ke jihar Katsina, Arewa maso yammacin Najeriya.
Sudai waɗannan bayin Allah, na zaune a cikin tsaƙa mai wuya, saboda fargabar rasa muhallansu da suke zaune ciki tare da iyalinsu inda suka zargi kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Najeriya watau TCN, a ƙoƙarinsa na inganta ƙarfin wutar lantarkin, da kafa manyan turaku na ƙarfe a cikin gidajensu tsawon shekaru 8 zuwa 10 kenan ba tare da biyansu kuɗaɗen diyyar wuraren yadda ya kamata ba.
A yanzu haka dai kimanim gidaje 300 ne a cikin wannan unguwa aikin ƙara ƙarfin wutar ya shafa, kuma da yawansu talakawa ne marasa ƙarfi, ciki harda masu buƙata ta musamman, amma kuɗaɗen diyyar da aka biyasu sun bayyana cewa wasu ko fili kuɗin ba zasu saya masu ba ballanta har a kai ga gina wani gidan.
Hasana Nuhu, uwa ce da ta ke da ƴaƴa 7 da mijinta ya mutu ya bari, ta ce ita gaba ɗaya ma an ce ba a ga sunanta ba a cikin jerin waɗanda za a biya diyyar dukda kuwa ƙaton ƙarfen turken wutar lantarkin da ta ce ya ratsa ta tsakiyar cikin gidan nasu da suka gada ita da ƴaƴanta.
Salisu Bello, wani bawan Allah da ya ke da lalurar gani, shima yana cikin mutanen da ke fuskantar wannan matsala, ya ce an bashi kuɗin naira dubu 66 kacal a matsayin diyyar gidajenshi guda biyu, ga shi kuma yana da iyali kimanin 20 a ƙarƙashinsa.
A yanzu haka dai wasu daga cikinsu saboda yanayi na rayuwa babu komai a cikin ƙuɗin da aka basu, wasu kuma sun ce an barsu da riƙon takarda a hannu, kuma daga ƙarshe ma an ce ba gidansu ba ne na wani mutum ne daban.
Duk wata hanya dai da mutanen nan zasu bi domin isar da ƙorafinsu, sun bita kamar yadda Habibu Kamilu Kankia ya bayyana mana, to amma dai a cewarsu har yanzu babu wani abu da aka yi don a tsamo su daga cikin matsalar, wanda hakan yasa suka yi kira ga gwamnati musamman gwamnan jihar Dikko Umar Raɗɗa da ya shiga lamarin nasu ko za a sama masu da mafita.
Saurari Rahoton A Cikin Muruat Da ke Ƙasa.
Kafin haɗa wannan rahoto, sai da Jakadiya ta tuntubi ofishin hukumar rarraba hasken wutar lantarki da ke Katsina domin samun ƙarin bayani, to amma dai shashen hukumar da ke kula da buƙatun al’umma ya bayyana cewa, ba su da damar da zasu yi magana akai sai sun samu umurni daga babban ofishinsu da ke Abuja.




