Wani matashi mai suna Idris a unguwar Babbar Ruga da ke jihar Katsina, ya rungumi sana’ar saƙa akurkin kaji da kwandunan shuka da na saka tumatur.
Matashi Idris, ya ce ya rungumi sana’ar ne saboda ya rufa wa kanshi asiri, ya kuma samu damar taimaka wa iyayensa da abinda zasu ci.
“Yanzu haka ina nan ina shirin yin aure da wannan sana’a, saboda ni da ita na dogara kuma ba ni raina ta.” inji shi.
Yace, “Da mutum ya je ya taɓa kayan wani ya ja wa iyayenshi abin faɗa gara ya kama sana’a ko yaya ta ke kar ya raina ta.”
Matashi Idris ya ce a rana yana saƙa akurki kamar uku haka ma akurkin kaji yana saƙa uku.
Saurari tattaunawar Jakdiya da matashin a nan ƙasa…
Daga ƙarshe wannan matashi ya yi kira ga ƴan uwanshi matasa da su tashi tsaye su nemi sana’a domin su rufa wa kansu asiri tare da taimaka wa iyayensu.



