Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Gabanin ziyarar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zuwa Jihar Imo a ranar Talata, Gwamnatin Jihar a ranar Asabar ta ƙaryata batun barazanar da Ƴan Ƙungiyar Rajin Kafa Ƙasar Biafra IPOB suka yi.
Kwamishinan yada Labaru da Dabaru na jihar Declan Emelumba a yayin wani taron da ya gudana a Owerri a ranar Asabar, ya bayyana cewa yan kungiyar Rajin kafa kasar Biafra, IPOB basu isa su dakatar da shugaban kasa ba.
Emelumba wanda yake mayar da martani kan gargadi da IPOB ta fitar, tana mai ayyana Dokar zaman gida a Jihar a ranar Talata, ya bayyana cewa jami’an tsaro a shirye suke akan ziyarar da shugaba Buhari zai kawo a jihar.
” Babu wanda ya isa yayi barazana ga Buhari. Shine Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Tsaro na Najeriya. Imo na ɗaya daga cikin jihar da yake mulka kuma yana da damar zuwa garin. Jami’an tsaro a shirye suke a kowane lokaci, kuma ina tabbatar maku da cewa zaiyi ziyarar sa cikin kwanciyar hankali da lafiya,” a cewar sa.
Kwamishinan ya bayyana cewa Buhari zai zo jihar ne domin ƙaddamar da muhimman ayyuka guda ukku da Gwamnatin Gwamnan Jihar Hope Uzodima ta shimfida.
Ya lissafa aiyukan da suka ƙunshi, kashin farko na hanyar Owerri zuwa Okigwe, sai hanyar Owerri zuwa Orlu da kuma sake ginannen wurin Majalissar Dokokin Jihar Imo.
Emelumba ya bayyana cewa ayyukan zasu kara habbaka tattalin arzikin da jindadin rayuwar al’ummar jihar, yana mai ƙara da cewa Gwamnatin jihar ta kashe Biliyoyin Nairori domin gudanar dasu.
Ya kuma bayyana cewa, ” Shugaban kasa zaizo domin ƙaddamar da buɗe hanyar Owerri zuwa Okigwe da hanyar Owerri zuwa Orlu da kuma sake ginin wurin Majalissar Dokokin Jihar a ranar 13 ga watan Satumba. Wannan sune manyan ayyuka da Gwamnatin Gwamna Hope Uzudinma ta gina.
“An kammala gina Majalissar Dokokin Jihar. An ƙyale ta Shekaru goma. Mambobin Majalissar suka bar wurin domin kula da lafiya, wanda alamu ne na rashin kyakykyawar damokuradiyya ba.
“An tsauara Jami’an tsaro. Babu wanda ya Isa yayi barazana ga Shugaba Buhari. Jihar Imo babu tashin hankali a cikin ta. Zamu karɓi Shugaban Ƙasa cikin nasara.”
