Jami’an Tsaro Ke Hana Ni Shiga Daji A Yaƙi Ƴan ta’adda Da Ni – Raɗɗa

Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana dalilinsa na ƙin cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na shekarar 2023 da ya ce in ya zama gwamna, tare da shi za a rinƙa shiga daji domin yaƙar ƴan ta’addan da ke addabar jihar.

Dikko Raɗɗa, a yayin wani shiri mai suna A FAƊA A CIKA da sashen Hausa na BBC ke shiryawa ne ya bayyana haka, bayan da aka saka wani hoton bidiyo na wani ɗan jam’iyyar adawa da ya ƙalubalanci gwamnan da ƙin cika wannan alƙawarin.

Raɗɗa ya soma da cewa akwai abubuwa da yawa da ba sai an bayyana wa mutane sun sani ba game da shirinsa na yaƙi da ta’addanci a jihar, amma ya ce ko kwanan nan auka cikin wani taro, sai da ya bi jami’an tsaro a karamar hukumar Safana inda suka samu nasarar kora wasu yan ta’adda da suka kai hari a lokacin.

Gwamnan ya ce, don ma yana samun tsaiko daga jami’an tsaro suna hana shi shiga dajin duk idan ya yi yunƙuri hakan.

Ya ce kwana biyu da suka wuce ya yi niyar bin jami’an tsaro a yankin Ƴan gayya inda ƴan ta’adda su ke amma jami’an tsaron soji suka tsare hanyar suka ce ba zai wuce ba.

Sai dai gwamnan ya ce sun bashi uzurin cewa a wannan lokacin babu cikakken shirin da za a tunkari ƴan ta’addan don haka dole ya haƙura ya dawo gida.

Dukda dai har yanzu ana fuskantar matsalar a jihar to amma dai a iya cewa ana samun rangwame bisa ga watannin baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *