Jonathan Ya Buƙaci A Tallafawa Matasan Afirka Da Guraben Karatu
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira da a baiwa hazikan matasan Afirka da ke fama da karancin kudin shiga na tallafin karatu.
Jonathan ya yi wannan kiran ne a jawabinsa wajen bikin yaye dalibai karo na 11 na Jami’ar Cavendish Uganda (CUU) a Kampala, da ke Uganda.
Jonathan, wanda shi ne Shugaban Jami’ar, a jawabinsa da ya bai wa Kamfanin dillancin abarai na Kasa NAN a Abuja ranar Juma’ar nan, ya tabbatar wa Jami’ar na ci gaba da bayar da goyon baya.
“Za mu ci gaba da mai da hankali wajen kawar da matsalolin samun damar zuwa manyan makarantu ga matasan Afirka da dama wadanda ke da hazaka amma masu karancin kudin shiga.
“Don haka za mu bukaci neman tallafin karatu ga matasa masu hazaka amma talakawa, ko da kuwa hakan na nufin hada su da tsarin rancen da za su biya daga baya,” inji Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriyar ya kuma bayar da shawarar yin hadin gwiwa tsakanin masana da masana’antu a nahiyar Afirka domin magance wasu matsalolin da yankin ke fuskanta.
