Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, ya koka kan tsarin Kotunan Najeriya, yana ma cewa babu adalci ko kaɗan a ciki.
Ya bayyana Najeriya a matsayin Ƙasar dake da ɓangaren Shari’a marar ƙarfi, wanda aka lalata ikon da yake dashi.
Gumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a yayin wani taro da aka shirya a maiduguri a matsayin wani ƙoƙari na maida tubabbun ƴan ta’addan Boko Haram da suka zuwa cikin Al’umma.
Ya ƙara da cewa,”Duk Wanda yake da wani sha’awa na Kasar mu, zai iya zuwa ya shiga aikin Soji.
“Miyasa muke barin yaranmu da jahilci? Miyasa akace ilimi ba na kowa bane? miyasa muke barin yawancin Al’umma da talauci?”
A lokacin da yake caccakar shuwagabancin siyasa na Najeriya, Gumi ya bayyana rashin jindaɗin sa na wasu ƴan Najeriya da suke tafiye-tafiye kan jiragen mallakin su.
Ya ce,”Wasu ƴan Najeriya na tafiye tafiye kan jiragen su kullum yayin da wasu yan Najeriyar basu san inda zasu saka yaransu domin suyi karatu a Makaranta. Akwai rashin Adalci.
“Idan kaje Kotu can ma babu adalci saboda karfin ikonta yayi kasa, yara suna nan ayi amfani dasu akan kowa”
