Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
An samu sabbabin mutane 74 da suka kamu da cutar Corona a jahar Ekiti.
Kwamishinan Lafiya na Jahar, Dr Oyebenji Filana, a cikin wata takardar Manema labarai a Ado Ekiti, ya bayyana cewa an samu sabbabin mutanen da suka kamu bayan kammala hidimar Babbar Sallah.
Dr Filana, ya Fadi cewa an samu raguwar mutanen da suke kamuwa da cutar, kuma akwai ƙarancin waɗanda aka killace, kafin Babbar Sallah, wadda aka gudanar a farkon wannan watan.
Kwamishinan ya bukaci mazauna jahar dasu bi dukkanin dukkanin Dokokin Kariya da Hukumomin Lafiya na Gwamnati suka sanya, domin hana yaɗuwar ta.
Dr Filana ya bada tabbacin cewa har yanzu allurar rigakafin itace hanyar magance cutar, ya kuma ƙarfafi mazauna da suyi Allurar.
Da yake tabbatar da cewa, kimanin Mutane 384,730 aka yiwa Allurar rigakafin a fadin jahar, kwamishinan ya bayyana cewa kimanin mutane sama da 80 aka horas tare da tura su wurare daban-daban, da kuma tawagar ma’aikatan lafiya 177 a kananan hukumomin Jahar.
