Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake fuskantar jinkiri a shari’ar da ya kai kotu yana neman diyyar Naira biliyan daya kan ICPC da wasu hukumomi, bayan da Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Maris.
Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta dage sauraron karar kare hakkin dan Adam da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shigar a kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da wasu mutane hudu zuwa ranar 25 ga Maris domin ci gaba da sauraro.
Mai shari’ar ta ce an dage shari’ar ne domin bangarorin da ke karar su gyara takardun da suka gabatar gaban kotu.
Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya shaida wa kotu cewa sun riga sun mayar da martani kan takardar ICPC, amma har yanzu ba su mayar da martani kan ta Sufeto Janar na ‘yan sanda ba.
A cikin karar, El-Rufai na neman kotu ta ba shi diyyar Naira biliyan daya, yana zargin cewa binciken da ICPC da wasu hukumomi suka yi masa tare da binciken gidansa ya saba wa hakkinsa na kundin tsarin mulki, ciki har da mutunci, ‘yancin kai da kuma sirrin rayuwa.
Tsohon gwamnan ya kuma roki kotu ta bayyana cewa sammacin binciken gidansa da wani babban alkalin majistare na Abuja ya bayar a watan Fabrairu ba shi da inganci, yana mai cewa an ba da shi ba tare da hujja mai karfi ba kuma yana dauke da kura-kuran rubutu da rashin takamaiman bayanai kan abubuwan da ake nema.
Sai dai ICPC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar, tana mai cewa jami’anta sun gudanar da binciken ne bisa sahihin sammacin kotu. Hukumar ta ce sun samu korafi a kan El-Rufai ne kafin su fara bincike, inda suka kai samame gidansa da ke Mambilla Street, Asokoro, Abuja, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda.
Haka kuma ‘yan sanda sun ce aikin binciken da suka yi ya bi dukkan ka’idojin doka, suna zargin El-Rufai da kokarin amfani da kotu domin kauce wa bincike da yiwuwar tuhuma.
Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai na hannun ICPC tun ranar 19 ga Fabrairu, bayan da a baya EFCC ta tsare shi na wasu kwanaki bayan ya amsa gayyata da ta aika masa.
