Ku yarda Da Kanku – Saƙon Buhari Ga Matasan Katsina
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ƙarfafi gwiwar matasan Katsina da cewa su yarda da kansu kan dukkan abinda suka sa gaba.
Buhari ya bayar da ƙwarin gwiwar ga matasan a yayin da ya halarci wani taro da ƙungiyar tuntuɓa ta jihar ta shirya da nufin yaƙi da tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
A bayaninsa a matsayinsa na uban taro, tsohon shugaban ya ce matasa su sani sune ƙashin bayan kowace al’umma don haka ya kamata su yarda da kansu da abinda su ke da kuma gobensu.
Buhari ya kuma gargadi matasan da su kauce wa shaye-shayen ƙwayoyi da sauran kayan da ke kauda hankalin mutum.
Hakazalika, ya yi kira ga iyaye da sanya ido ga yayansu domin samun al’umma ta gari.
