Kungiyar CAN ta yi wa Gwamna Uba Sani, addu’a

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Kaduna ta yabawa Gwamna Uba Sani kan yadda yake sauraron jama’a da kuma cika alkawurran da ya dauka tun bayan hawansa mulki, tare da yi masa addu’ar Allah ya kara masa hikima wajen jagorantar jihar.

Shugaban CAN na jihar, Rev. Caleb Ma’aji, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da gwamnan ya karbi bakuncin shugabannin Kiristoci domin bude baki na watan Ramadan a Fadar Gwamnati. Ya ce a bara sun roki gwamnan ya dawo da daukar nauyin aikin hajjin Kiristoci zuwa Urushalima wanda aka dakatar tun 2015, kuma a bana mutane 49 sun riga sun je kuma sun dawo daga tafiyar ibadar.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta fara gina wasu manyan hanyoyi da kungiyar ta nema a Kaduna, yayin da Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa dawo da tallafin aikin hajjin Kiristoci ya dace da manufofin gwamnatinsa na adalci da daidaito, yana mai rokon shugabannin addinai su ci gaba da mara masa baya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *