Kwamitin yaƙi da ƙwayoyi ya shiga neman haɗin kan EFCC

Kwamitin yaƙi da ƙwayoyi ya shiga neman haɗin kan EFCC

Kwamitin Kar Ta Kwana na Yaƙi da Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi na Jihar Kano ya nemi Hukumar EFCC ta haɗa hannu da shi wajen dakile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma laifukan da ke da alaƙa da harkar.

Shugaban kwamitin, Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Mukaddashin Daraktan EFCC na Shiyyar Kano, ACE1 Friday Ebelo. Ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da masu safarar ƙwayoyi, tare da tallafa wa masu fama da shaye-shaye domin su koma cikin al’umma.

A nasa ɓangaren, Friday Ebelo ya ce EFCC za ta ba da gudunmawa wajen wannan yaƙi, musamman saboda alaƙar da ke tsakanin safarar ƙwayoyi da kuɗaɗen haram. Ya buƙaci kwamitin ya riƙa tura wa hukumar bayanan sirri kan masu ɗaukar nauyin safarar miyagun ƙwayoyi domin a gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *