Kwankwaso Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ba Zai Yarda Ya Zama Mataimakin Ɗan Takara

Kwankwaso Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ba Zai Yarda Ya Zama Mataimakin Ɗan Takara

Dan Takarar shugaban kasa na jam’iyya mai alamar kayan marmari wato (NNPP) , Rabi’u Musa Kwankwaso, a ranar Asabar , ya bayyana cewa in ya yarda ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na wata Jam’iyya to jam’iyyar sa ta NNPP rushewa za ta yi.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake ganawa da manema labarai, bayan ya halarci bukin bude Babban ofishin jam’iyyar NNPP a jahar Gombe, ya kuma gana da sauran zababbun membobin kungiyar.

Tsohon Gwamnan na Jahar Kano, ya fadi cewa, cikin kankanen lokaci jam’iyyar NNPP tayi suna, duk wani abinda zai kawo rashin sa na zama Shugaban kasa shine zai kawo rushewar jam’iyyar.

Kwankwaso ya kuma tabbatar da cewa, jam’iyyarsa ta tattauna da jam’iyyar Labour Party akan cewa su dunkule su zama daya, amma babbar matsalar da ta kawo rashin faruwar hakan shine wanda zai zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Ya bayyana cewa, ” tun daga lokacin da suka fara tattaunawa da jam’iyyar Labour Party, babban abin shine wanene zai zama shugaba idan jam’iyyun biyu sunyi maja.

” Daga karshe kuma wasu daga cikin wakilanmu su kayi tunanin cewa ya kamata ayi amfani da shekaru da matsayin karatun da mukaman da mutum ya rike da kuma yanda ya gudanar dasu, da dai sauran su. In ji shi.

“Tabbas wani bamgaren basu yarda da hakan ba , da yawa daga cikinsu sun yarda da cewa, ya kamata shugaban kasa ya fito daga yankin kudu maso gabas.

” Idan na yarda na zama mataimakin wani dan takarar shugaban kasa a kasar nan, to jam’iyyar NNPP zata rushe, saboda jam’iyyar na tafiya ne akan yadda muka ginata na tsawon shekaru talatin. In ji Kwankwason.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *