Majalisa ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala Biliyan 6

Majalisar trayya ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na karɓar rancen dala biliyan 6 daga ƙasashen waje domin aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Bukatar ta kunshi rancen dala biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma dala biliyan 1 daga UK Export Finance ta hannun Citibank na Landan.

Shugaban ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen aiwatar da kasafin kuɗi, gina muhimman ababen more rayuwa, da kuma biyan wasu basussuka masu tsada.

Bayan nazari da gabatar da rahoto daga kwamitin kula da basussuka, Majalisar ta amince da bukatar, inda ta bai wa shugaban ƙasa damar ci gaba da karɓar rancen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *