Mangal ya sa an yi wa wani mutum tiyata kyauta bayan shafe shekaru takwas da ciwon mafitsara

Mangal ya sa an yi wa wani mutum tiyata kyauta bayan shafe shekaru takwas da ciwon mafitsara

Wani majinyaci daga Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina, Yusuf Umaru, ya samu tiyata kyauta ta kimanin Naira miliyan daya, bayan shafe shekaru takwas yana fama da ciwo da matsalar mafitsara.

Umaru, wanda ya bayyana haka yayin da za a yi masa tiyatar a Asibitin Kwararru na Kasusuwa na Amadi Rimi da ke Katsina, ya ce matsalar ta jefa shi cikin radadi tare da kawo cikas ga ayyukansa na yau da kullum tsawon shekaru.

Ya ce ya taba neman magani a wasu asibitoci, amma an bukaci ya biya kimanin Naira 700,000 kudin tiyatar kadai, yayin da sauran kudade da suka hada da magunguna, wasu hanyoyin jinya da kudin kwanciya a asibiti suka kai kimanin Naira 300,000.

A cewarsa, matsalar yin fitsarin cikin sauki ta kara tsananta masa rayuwa, yayin da kudin samun kulawar likitocin kwararru suka gagari karfinsa.

Ya ce halin da yake ciki ya sauya ne bayan an gano shi a matsayin daya daga cikin wadanda za su amfana da shirin bayar da tallafin lafiya kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi a Katsina.

Umaru ya bayyana jin dadinsa da godiyarsa ga gidauniyar, yana mai cewa tallafin ya dawo masa da fata bayan shafe shekaru yana rayuwa cikin radadi.

Ya ce tallafin ba wai kawai ya rage masa nauyin biyan kudin tiyata ba ne, har ma ya ba shi damar samun kulawar kwararrun likitocin da ya dade yana bukata.

Haka kuma, Khadija Abdullahi, wata mai amfana da shirin, ta ce diyarta ‘yar shekara biyu ta yi fama da hydrocele, wato kumburin da ke tattare da ruwa a kusa da maraina, na tsawon kusan shekara guda.

Abdullahi ta ce rashin karfin tattalin arziki ya hana iyalinta samun damar biyan kudin tiyatar, tana mai bayyana fatan cewa shirin zai taimaka wajen dawo da lafiyar diyarta.

Wata mahaifiya da ta yi magana a madadin danta, Isma’il Bishir, mai shekaru 15, ta ce yaron ya dade yana fama da radadin matsalar duwatsun koda.

Ta ce iyalinsu ba su da karfin biyan kudin magani saboda halin da suke ciki na rashin kudi, lamarin da ya sa matsalar ta kara tsananta kafin a shawarce su da tuntubar Gidauniyar Mangal.

A cewarta, bayan tuntubar gidauniyar, an sanya wa danta lokacin gudanar da tiyata.

Ta yabawa gidauniyar bisa samar da maganin kyauta, tana mai cewa tallafin ya kawo sauki ga iyalinta bayan dogon lokaci na fama da matsalar.

Da yake magana, Mista Hussaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, ya ce zuwa yanzu akalla majinyata 2,160 sun amfana da shirin, yayin da ake sa ran kula da wasu kusan 120 a wannan zangon.

Kabir ya ce shirin na daga cikin ayyukan jin kai na gidauniyar a fannin kiwon lafiya, musamman domin taimakawa marasa galihu da ke bukatar kulawar lafiya amma ba su da karfin biyan kudin magani.

Ya ce manufar shirin ita ce inganta damar samun muhimman ayyukan kiwon lafiya, musamman ga marasa lafiya da ke fuskantar matsalar rashin kudin kula da lafiyarsu.

Kabir ya yi kira ga masu hannu da shuni, kungiyoyi masu zaman kansu da jami’an gwamnati da su yi koyi da irin wannan kokari, ta hanyar tallafawa ayyukan da za su inganta damar samun kulawar lafiya.

Ya ce irin wadannan shirye-shirye za su taimaka wajen bunkasa kokarin gwamnati na samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga marasa galihu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *